Go Back
Communicating for Change

Document Body Page Navigation Panel

Pages 1--15


Page 1 2
1
July, 2000 (Hausa) CHANGE Radio
Aiyukan raya kasa:
BALA' I:
Ambaliya ta shafi kudancin somaliya. 1min. 37secs. 4 Ruwan da ake doukin samu a kudanoin Somaliya,

yazo har ya fara gyara ga jama'a bayan ma tsalolin da sukayi fama dasu na kamfar ruwan.

TATTALIN ARZIKI:
Kungiyar turai ta naira miliyan 100 domin
kungiyoyin ma' aikata a najeriya. 1min. 18secs. 4
Kungiyar Turai da Gidauniyar Jamus zasu kashe dala

miliyan daya domin gina kungiyoy: ma' aikata a Najeriya.
Kudi-kudi kudi. 3min. 8secs. 6
Wata kungiya mai zaman kan kanta tana namijin kakari domin yankuna mafi talauci na Najeriya domin

samun nasara ta hanyar wasu shirukan kamfanoni.
Kasahen kungiyar acp/ eu zasu sanya hannu bisa
2min. 2secs. 10
sabuwar yarjejeniya a watan yuni wadda zata kawo karshen yarjejeniyar lome.

KIWON LAFIYA:
Kenya zata bullo da darusan kare cutar
kanjamau a manhajojin cibiyoyin ilmi. 1min. 11secs. 4
Darektan ilmi na Kenya ya bada sanarwar za a bullo

da manhajar kare cutar kanjamau a dukkan cibiyoyin ilmi na kasar.

Watakila kofi ya kare kwalwa daga cutar kyarma. 1min. 24secs. 6 Sabon bincike ya kawo shawarar shan kofi zai
taimaka wajen kare kamuwa da cutar kyarma.
Wata kwayar maganin haihuwa ta kasa samun nasara. 1min. 38secs. 8
Masu bincike sun gano cewar kwayar magance rashin haihuwa ga mata zai taimakawa mata ba.

Wani sabon da aka bullo dashi na iya taimakawa masu da cutar sankara. 1min. 9
Bisa la' akari da kwayoyin hallita, wani sabon magani na iya taimakawa masu fama da cutar sankara.

Kiwon lafiya mai kyau ko ina a duniya. 1min. 59secs. 10 Maganar kiwon lafiya mai kyau a duniya itace zata
mamaye ajandar taro na 53 kan kiwon lafiya a duniya na Genava.
1
1 Page 2 3
July, 2000 (Hausa) CHANGE Radio
2
FASAHA.
Cigaban na'urar e-mail na barazana ga Amurka. 1min. 32secs. 9 Wata sabuwar na'urar komputa na yaduwa

cikin hanzari ta na'urar E-mail.
Muhalli YANAYIN MUHALLI.

Taron karawa juna sani kan dokar dokar filaye a najeriya. 2min. 15secs. 5 Taron karawa juna sani zai maida hankali kan filaye ta 1978
a Najeriya wanda wasu da dama tafi dadadawa yanayin muhalli.
Masu kare masu kare muhalli na makokin karewar dazukan amazon. 1min. 2secs. 7
Masu kula da muhalli na Brazil sun fara barkanci game da jana'izar gandun dazukan Amazon domin
gargadi bisa yunkurin fadada gonaki a dazukan.
Gwamnati tayi gargadi a Nairobi game da kareware wasu nau'o'in dabbobi. 1min. 30secs. 7
Bisa kiyasin dabbobi da itace iri-iri har 31 dake karewa a duniya Gwamnatoci sun himmatu wajen ceto
wadan nan halittu a duuiya.
DABBOBIN DAWA:
Turare da kimiya sun taimaka wajen ceto damisa. 2min. 1sec. 5 Dabbar nan da tafi kowace dabba gudu a duniya

tana fuskantar karewa, amma wani shiri da aka
gudanarwa zai taimaka wajen ceto su.

Na'uin dabbobi 138 dake jerin adanda ke fuskantar hatsarn karewa. 2min. 21secs. 8
Masu kula da kare hallitu na kira da a kare wasu
na'o' in dabbobi dake fuskantar barazanar karewa a duniya.

Hukumar wwf ta bukaci hada karfi domin ceto dabbobin dake kurmi. 1min. 54secs. 9
Hukumar kare halittu ta duniya ta kukaci taron
kare muhalli da ya dauki matakan da suka dace domin kare dabbobin dake zaune a kurmi daban -daban a duniya.

Abubuwan dake faruwa a duniya:
Batun kyoto cikin ajanda: 48secs. 11
Taron jam' iyu zai tattauna kan amincewa da wannan batu na duniya.

Taron kasashen Afrika kan kula da albarkatun kasa. 44secs. 11 Burkina Faso zata karbi bakwancin babban taro
cikin watan Yuli.
2
2 Page 3 4
3
July, 2000 (Hausa) CHANGE Radio
Sharhin editoci da labarai a takaice. 35secs. 11
Yobe zata kafa dokar hana farautra da sare itatuwa. 59secs. 12
Sa rai ga wadanada suka fidda rai. 1min. 42secs. 12
Sashin yara:

Najeriya zata karbi bakwancin taron yara kan kafofin yada labarai, wanda za' ayi a kasar Girka. 1min. 40secs. 12

Yadda agwagwan-ruwa ta sami zanen bayan ta. 1min. 31secs. 13 Fushin da kabilar bushman yayi ya sanya agwagwan
ruwa ta sami da' irar dake bayan ta.
Lesenga da gwayaye: 1min. 51secs. 13
Yadda matashi ya koyi darasi kan rashin kidaya kwayayen sa kafin kyenkysa.

Karin magana:
karin maganganu kan muhalli da raya kasa. 14 3
3 Page 4 5
July, 2000 (Hausa) CHANGE Radio
4
labaru
Ambaliya ta shafi kudancin somaliya. 1min. 37 secs. Ruwan sama da ake jiran saukar sa a kudancin Somaliya ya sauka. Saidai abin takaici ruwan ya fara
gyara, har yakai ga yin ambaliya a kauyuka da garuruwa, wanda hakan ya kara jefa jama'ar da sukayi fama
da shiga wani jafa'in.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarun Najeriya ya ruwaito, kogin Juba, wanda shine mafi girma a Somaliya dakuma kogin Shabella sun jefa jama'ar dake zaune a gabar su cikin tasku. Ambaliya daga kogin Jubba
tayi mummunar ta'adi a gari mai tashar jirgin ruwa na kismato ta yadda ambaliyar ta datse hanyar da ta
hade garin da babban birni kasar Mogadishu.

Dukkan zurga-zurgan kasuwanci tsakanin da kismota ta hanyar terra duk sun tsaya a sakamako karin ambaliyar . wanda akayi akan idon sa ya shaiddawa gidan rediyo VHF dake jilib cewa daruruwan gonaki
dake bakin kogi ne akayi watsi dasu bayan da kogin na juda ya cika ya tumbatse. Hakan abin ya kasance
ma shekaru uku da suka wuce lokacin da akayi mummunar ambar ambalayar ruwa a kudancin na somaliya. Sama da iyalai dari shida ne suka bar gidajen su, wadanda yanzu haka suna warwatse a yankunan chetoh

da kuinsdishe.
Gwamnan lardin Hawlwadag, Hassan Adbullah yace mutanen da suka wahala daga cutukan zazzabin cizon
dakuma kolera bazasu iya jurewa tagayyara kuma ba. Ya kara da rokon samun taimakon gaggawa domin ceto jma ar sa dake mutuwa saboda rashin abinci da wurin kwana magunguna.

The Guardian.
Kungiyar turai ta ware naira miliyan 100domin kungiyoyi a Najeriya. 1min. 18secs.
kungiyar kasashen Turai zata kashe dala miliyan daya wajn aikin sake gina kungiyoyin ma'aikata a Najeriya. Shugaban kungiyar kwadago ta kasar yace daga cikin adadin kukin dala dubu 90 zai fito ne daga

kungiyar kungiyar kasashen Turai yayinda ragowar dala dubu dari kuma wata gidauniyar kasar Jamus mai suna Friederic Ebert Stifund.

Kamar Yadar Yace za ayi akiki da kudin a fanoni bakwai, wadanda suka hada da kafa kungiyoyin kare demokuradiya, karfafa harkokin binciken kimiya da labarai dakuma kula da aiyuikan kungiyoyin. Ya kara
da cewa aikin shine na farko tsakanin Najeriya da kungiyar kasashen Turai domin bunkasa harkokin kungiyoyin ma' aikata a matsayin su na jigogin demokuradiya.

Wakilin gidauniyar a Najeriya Mr. Shwenzesky yace kungiyoyin ma' aikata sun kamaci samun taimako daga waje domin zama bisa matsayin su dakuma samun gajiyar da ta kamata kan harkokin da suka jibanci
na Gwamnati. The Guardian:

Kenya zata bullo da manhajar cutar kanjamau a makarantu. 1min 11secs. Za a bullo da manhajar kula da cutar kanjamau daga makara tun Firamare zuwa kwalejoj nan gaba kadan,
kamar yadda darektan ilmi na kasar Sammy Kyungu ya fadi. Darektan yace ma'aikatar ilmi ta gudanar da kosa-kosai ga Malami ta yadda zasu iya tafiyar da wannan aiki yadda yakamata.

Ma'aikatar ta dauki wannan mataki ne saboda la'akarin da Gwamnati tayi kan wayarwa da jama'a kai game da illar mugunyar cutar a makarantu, tun cikin watan Oktoban bara. Darekta ya cigaba da cewa
ma'aikatar tana tara rahotani kan yawan marayun da iyayen da suka rasa iyaye a sanadiyar cutar kanjamau, danufin samar da kudin ilmantar dasu. 4
4 Page 5 6
5
July, 2000 (Hausa) CHANGE Radio
Da matsalar tattalin arziki kamata yayi makarantun Gwamanti suyi la' akari da halin da yaran talakawa ke ciki, domin kaucewa korar su daga makarantu saboda rashin rashin biyan kudin makaranta inji Kyungu.

Sama da kashi 12 cikin 100 na mutanen da shekarun su ke tsakanin 15 zuwa 49 ne ke dauko da kwayoyin
cutar HIV a kasar Kanya. Kimanin yara dubu dari daga cikin yara miliyan 2 da kiyasta suna dauke da kwayoyin cutar suna kasar Kenya.

Daily Nation.
Taron karawa juna sani kan doka da manufar filaye a Najeriya: 2 mins 15 secs.
Kwanan nan ne kungiyar da muhalli da karkara ta 2000 (CCDI) ta shirya taron karawa juna sani game da manufofi da dokar filaye a Najeriya. An gudanar da taron ne awata cibiya da ake kira Goethe a Lagos,

inda wadanda sukayi jawabi da wadanda suke halarta suka fito daga sassa daban-daban na rayuwa musamman lauyoyi da' yan jaridu da masana ilmi da kungiyoyi masu zaman kansu. Taron yafi maida
hankali ne kan dokar amfani da filaye ta shekarar 1978, wanda ta baiwa Gwamnati ikon mallakar filaye a
Najeriya.

Irin wannan abu kuwa bawai kawai ya gurgunta raygunta rayuwar al'uma ba yama dagula daukacin tsarin zamantakewa. Kamar yadda shugaban kungiyar ta CCDI 2000 Mr. Ako Amadi ya fadi duk da cewa
hanshakan kamfanoni suna tsotse albarkatun Najeriya ne bayan da aka zartar da ita wannan dokar a
1978. Babbal illar dokar kan yankunan dake da ruwa suma an tabo batun su a taron.

Mahalarta taron sun yarda da cewar dokar, wadda ba asake nazarin ta ba tun lokacin da aka ta, kamata yayi a soke ta ko kuwa ayi mata gyarar fuska. Kungiyoyi masu zaman kansu, sume sun gabatar da bukatar
su ga CCDI 2000. Kungiyar kuma tana bada kwarin gwiwa kan irin wannan aikin. CFC.

Turare da kimiya sun taimake wajen karuwar damisa: 2 min secs. Nau' in Damisan nan akeyiwa lakani karta kwana yanzu haka sun tasamma karewa a duniya baki daya.
Domin kuwa irin wadan nan damisan suna mutuwa ainun a daji dama wadanda ake ajiya dasu a gandun dazuka domin suna fuskantar matsalolin karuwa.

Duk da hake yanzu an bullo da wani shiri na musamman wanda zai inganta karuwar su. Daga cikin shirin harda kyautata zaman su dakuma amfani da wani irin turare wanda zai janyo hankalin namijin damisa zuwa
ga macen domin yin barbara.
Masana kimiya sun dade da sanin shekaru da dama kenan irin wadan nan nau'in damisa ke ta mutuwa a dazuka, haka kuma wadanda ke ajiya a gandun daji suma saidada raguwa sukeyi. A 1998 akalla irin
wadan nan damisar 40 ne suka mutu a Arewacin Amurka wasu saboda tsuffa wasu kuma a sanadiyar wata cuta mai kama da kanjamau. Yanzu 250 ne kadai na irin wadan nan dabbobin suka rage a nahiyar.
Amma akwai wasu 'ya' yan damisan guda hudu, wadanda dasu ne ake kokarin gudanar da wannan shirin
a gandun daji na San Diego.

Wani ma'aikaci a gandun dajin Susan Millard Davis yace irin wadan nan damisan mata sun daina bukatar saduwa da maze, domin haka suke kokarin ganin sun samo hanyar janyo jankalin matan damisan domin
saduwa da maza. Anyi amfani da wata allura a wannan gandun dajin kuma tayi amfani.
Haka kuma ana kokarin kara kyautata rayuwar damisan dake dazuka ciki harda sama musu wuraren kadaicewa. Misali a San Diego wata damisar ta haihu yayinda aka kebe mata wuri nata na musamman
kimanin mil guda daga sauran dabbobin kuma nesa daga wurin da mutane suke. Tunda shike damisa tafi 5
5 Page 6 7
July, 2000 (Hausa) CHANGE Radio
6
son zama ita kadai a dajim wata hanya kulawa da ita itace na ajiya namijin damisa daban da ita damisar, Masu bincike kuma sai su hada su sau daya a shekara a daidai lokacin yin barbara.
Damisa tana kan hanyar karewa ada can kafin aka dauki matakin sake maido dasu. Amma yanzu ganin 'yan kalilan ne suka rage, rashin kula dasu na kashe kwayoyin halittun su, wanda ke sanya suna saurin
kamuwa da cutuka. Yanzu haka dai damisan kar ta kwana 12,0000 ne kadai suka rage a duniya. Cnn.

Kudi-kudi-kudi. 3 min 8 secs. Gidauniyar habaka kasuwanci (GBF) daya daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu a Najeriya tayi taron
ta kan hakkin manyan kamfanoni ga zamantakewar jama'a cikin watan Mayu. Makasudin kungiyar ta GBF shine hade mafiya talauci a Najeriya da manyan kamfanoni masu arziki ta hanyar samun rance.
Bankin UBA ne ya dauki nauyin taron, wanda kuma wakili daga ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan tattalin arziki da cibiyar bada rance (MFI) dakuma cibiyar raya kasa, wanda ta baiwa mata manoma
rance a Arewacin Najeriya.
Babbar darektan GBF Mrs. Ndidi Nnoli Edozie ce ta fara bude taron da jawabi tare da sako game da kudi, wanda tace kudi da kowa ke hankoron samu amma komai yawan su in ba anyi amfani dasu ba to
basa tsinana komai game da rayuwa. Shima babban darektan UBA, Alhaji Abba Kyari ya bukaci sauran bankuna da su taimakawa marasa abin hannu a Najeriya. UBA ta ware naire miliyan 90 domin bada jarin
rance ga masu karamin karfi ta hannun kungiyar GBF. Shugaban hukumar UBA Kalu Uke Kalu ya marawa hangen nesan Bankin kana ya bada haske kan yadda bankuna yanzu suke tafiyar da aiyukan su tsakanin
masu shi da marasa shi. Yayi bayanin cewa yayinda manyan kamfanoni ke biyan kudin ruwa tsakanin kashi 15 zuwa 20 cikin dari, kananan masu masana' antu da marasa galihu na biyan kudin ruwa na tsakanin 20
zuwa 40 cikin dari, domin haka Kalu Uke Kalu ya bukaci bankuna da su sake lala domin ganin dari, domin
haka Kalu Uke Kalu ya bukaci bankuna da su sake lale domin ganin arzzikin Najeriya yakai ga kowa da kowa wanda hakan shine zamen lafiya da kwanciya hankalin kasar baki daya.

Mrs. Edns James Ishaya babbar darektan cibiyar raya kasa, ta bada labari mai karfafafa gwiwa kan yadda rancen da kungiyar ta baiwa mata suka kuma biya cikin lokaci. Ta fafi yadda mata manoma da suka sami
bashin da ya kamata daga naira dubu daya zuwa dubu biyu, sun sami ribar da yakai kashi 300 zuwa 400 cikin dari wanda hakan ya kara inganta rayuwar su. Mrs. James Ishaya ta kammala da cewa tana fata
GBF ba zata cigaba da samun taimako daga kasashen waje ba saidai manyan kamfanoni da bankuna a Najeriya, wadanda suke da sha'awar ganin sun tallafawa marasa galihu.

Babba aikin GBF shine jan hankalin manyan kamfanoni su taimakawa matalauta tare da tabbatar da cewar 'yan Najeriya ne zasuyi maganin matsalolin dake ci musu tuwo a kwarya na game da aiyukan raya kasa.
Yanzu haka kungiyar na goyon bayan shirin sarrafa shara dakuma aiyukan samar da rance na Ikenne, da masana' an tar sabulun salo a Awe. Sauran aiyukan sun hada da na Inshoran kananan masana' antu ta
hanyar kamfani Inshora na Aiico.
GBF yanzu haka tana samun taimako daga bankin UBA da hukumar Waterhouse da Mobil da Chevron da Aiico da sauran wasu kungiyoyin.
CFC.

Kofi dake kare cutar makyarkyata: 1min 24 secs. Wani bincike da mujallar likitocin Amurka ta buga ya nuna cewa kofi na iya magance kamuwa da cutar
makyarkayata. 6
6 Page 7 8
7
July, 2000 (Hausa) CHANGE Radio
Tawagar masu binciken sunyi nazari kan Japanawa da Amurkawa sama da 8000 na tsawon shekaru 30 kuma sun gano cewar wadanda suke dirkar kofi fiya da kofi uku a rana suna da juriyar kamuwa da cutar
har sau biyar fiye da wadanda basa sha. Cutar makyaryata, wata irin cuta ce dake nakasa jijiyoyin dake zuwa cikin kwalwa. Kwayoyin suna lalata
jijiyoyin ta yadda mutum ba zai iya tsaya kurum ba sai ya rinka yin makyarkyata, wasu ma suna kaiwa ga tabuwar hankali.

Koda yake ba afayyace wannan bincike ta hanyar kimiya ba, saidai ana zato koffi na taimakawa wajen kare aukuwar kamuwa da cutar, dake lalata kwalwa.
Koda shike binciken yayi la'akari da wasu dalilan dake sanya kamuwa da cutar kamar su shan taba, lokaci baiyi ba da za a shawarci jama'a yin amfani da koffi wajen magance cutar ta makyarkyata. Masu
binciken suna fata nazarin zai kai ga wasu binciken kan hanyar da tafi dacewa domin karewa dakuma magance cutar.
CNN.
Masu kare dazuka suna makokin mutowar dajin amazon. 1min 2secs. Masu kare dazuka a Brazil sun fara bukin jana'izar mutuwar dajin Amzon na bogi danufin nuna cewar
hankoron fadada aiyukan nona a yankin na illa ga wannan daji.
Daruruwan masu makoki dauke dauke da makara suka bi ta gandun dajin Ibirapuera dake Sao poalo suna matse irin itacen nan na Ikpe domin nuna rashin amicewar su da kokarin da akeyi na gurbata wannan
katafaren daji mafi girma a duniya. Wannan kuwe yabiyo bayan irin nasarar da masu kare dazukan suka samu ne a makon da ya gabata inda majalisar dokokin Amurka tayi watsi da shirin dokar sare wani
bangare na gandun dajin Amzon da aka kare zuwa kashi 50 daga kashi 80 cikin dari a watan Mayun da ya shige.

Dajin Amazon wanda ya nunka kasar Faransa sau biyu nan kashi hamsin cikin dari na iri-iren itatuwa da halittu na duniya ke zaune. A bara saida akayi asarar filin dajin da yakai fadin jihar Hawaii domin aikin
katako da noma. Reuters.

Gwamnatoci sun yi shela game da karewar dabbobi da itatuwa a taron nairobi. 1min 30 secs.
Raguwar yawan su kawai abin tsoro ne. Kamar yadda shirin majalisar dinkin duniya kan muhalli raguwar halittu tun daga shekarar 1600 yana karuwa 10,000 da zai ninka.

A yan akwai dabbobi da itatuwa iri-daban-daban har 31,000 dake fushantar zuwa 10,000 da zai ninka.
Bisa wannan barazana ce Gwamnatocin kasashe 177 suka tura wakilan su a taron kula da halittu a Nairobin Kenya, domin gyara dangantaker dake tsakanin dan adam dakuma raguwar halittu.

Babban darektan shirin kula da muhalli na majalisar dinkin duniya, Klaus Teepfer yace irin yadda yawan karuwar jama'a ke aukuwa ba gibgibtawa, dakuma halakar da halttu, ya zame babu zabi illa a samo wata
dabara cikin hanzari domin kaucewa irin yadda ake halakar da irin wadan nan halitun.
Wanda aka kaddamar a taron koli kan duniya a Rio dejeneiro a 1992 shine ya haifar da taron kula da halittu da akayi a shekarar 1998. 7
7 Page 8 9
July, 2000 (Hausa) CHANGE Radio
8
Taron wannan shekara zzaiyi nazari kan irin cigaban da kasashen suka samu wajen magance barazanar karewar halittun. Babban burin taron shine samo hanyar da za a bi wajen aiwatar da shirin a ko in a duniya
dakuma yankunan kasashe. ENN.

Maganin viagra bai sami nasara ba kan taimakawa mata: 1min 38 sec. Yayinda har yanzu ake tababa game da amfanin maganin Viagra, wanda ke magance rashin haihuwa ga
mata, ana kuma cigaba da bincike kan ingancin sa. Mutance da dama suna ikirarin rashin hainuwa babbar cuta ce da ta kamaci samun kula ganin yadda ya shafi karuwar jama'a dakuma kare yanain dan adam.
Yayinda mahawara ke gudana kwayar maganin kanta ta kasa samun nasara bisa gwajin da akayi kanta game da mata. Wannan kuwa ya biyo bayan nazarin da akayi ne wanda kamfanin magunguna na Pfizer ya
dauki nauyi wadanda kuma shine ya samar da maganin.
Sakamakon nazarin da aka gabatar da wata kwaleji dake Amurka dakuma wata cibiya a San Francisco.
Ya tabbatar da nazarin da akayi karami tunda farko, wanda shi wannan maganin bai taimakawa matan da basa haihuwa ba wajan samum 'ya'ya.

Viagra, wanda shine magani na farko da akayi domin samar da haihuwa ya biyo bayan amincewa da akayi ne a Amurka a shekarar 1998. Maganin yayi cinikin sama da kudi dala miliyan dubu daya a bara kuma
kamfanin pfizer yana fatar kara samun riba ta hanyar samun likitoci su rika baiwa mata shawara domin aiki da kwayoyin.

Nazari na bayan nan duk da haka ya sanya fatar da akeyi ta dushe, domin daga cikin mata 583 da akayi gwajin maganin wadanda suke da matsealolin haihuwa Viagra baiyi musu siki ba yadda ake zato.
Desert News /CFC.
Halttu 138 a duniya suna daga cikin masu hatsarin karewa: 2mins 21 secs. Sama da halittu 130 daga cikin halittu 600 a duniya suna cikin jerin masu hatsarin karewa daga doron
duniya. Wadan nan halittu sun hada daga duwatsu da goggon biri dake tsakiyar Afriika inda yayi yayi
kamari, domin kashe su da akeyi wajen yin tsafi dakuma saidawa domin ci. Saidai kuma mazauna yankin sun kasa sanin hakan na da matukar illar dakuma barazana ga irin wadan nan halittu.

Tilas ne a kare wuraren da irin wadan nan halittu suke domin rayuwar su inji Russell Mittermeire kwarare kan harkonkin halittu kuma shugaban cibiyar kula da yanayi ta duniya. Yana daga cikin kwararu 400 da
sukayi taro a gandun dabbobi na Broodfield kusa da Chicago domin tattaunawa kan halittu dakuma rayuwar su.

Daga cikin dabbobin dake fuskantar barazanar harda birren bambo da manyan goggon biri wadanda ake samun su kadai a jumhuriyar Demokuradiyar Congo. Yanzu haka biren bambo ana ritsawa dasu a yakin
da akeyi a kasar ta Congo. Wasu ana kashe su domin samun nama ga' yan dugun hijira dake da yawan dabbobin daji daban-daban, wanda kuma biran dake tsaunuka da goggon birin dake kasa a dajin okapi
duk suna fuskantar wannan barazanar ciki harda ragumin dawa.
Masu bincike sunce samun karumar birai zaiyi nawa domin wasu nau'in birran basa wuce 'ya'ya uku kacal
a rayuwar su.

Haka kuma cinikin irin wadan nan dabbobi ba bisa doka ba dakuma wutar daji da aka yi shekaru biyu anayi a oranguntas dake yankunan Sumatra da Borneo a Indonesiya ya sanya ana asarar su kimanin 1,000
kowace shekara, kuma an kiyasta abinda ya rage yanzu bai shige 6,000 ba,. Bornce ta gurgunce da wutar 8
8 Page 9 10
9
July, 2000 (Hausa) CHANGE Radio
daji a shekarun 1997-98 inda irin wadan nan dabbobi suka rage tsakanin 10,000 zuwa 15,000 abinda aka da irin su 60,000 a shekarar 1980.

Sauran nan'o'in birran dake fuskantar barazanar karewa sun hada da masu jikin zinari dake gabar tekun
Brazil da masu yawan gashi dake paru dakuma wasu dake Madagascar. CNN/ Reuter.

Wani sabon magani dake iya dakatar da cutar sankara: 1min. Wani sabon magani da akayi domin da cutar sankara da akayi wanda ke aiki bisa kwayoyin halitta kwalliya
zata biya kudin sabulu kan gwajin farko da akayi. Maganin ya taimaka wajen dakile yaduwar kwayoyin
cutar dake haddasa sankara.

Koda shike har yanzu ana matakin farko ne na maganin da akayiwa lakanin IMG-C225 yayi aiki ga wani mai fama da cutar a kai dakuma wuya, wanda ya kasa samun sauki a magungunan da akayi masa an
baya. Shi kansa maganin ya nuna yana iya dakile karuwar cutar wanda ada suke keruwa. Yazuwa yanzu
dai dukkan nazarin da akayi sun nuna cewa maganin na amfani wajen dakile yaduwar cutar ta sankara. Fata anan shine na ganin dukkan aiyukan maganin an ta'allake su ga DNA dakuma gwaje-gwaje kamar

yadda likitoci suka baiyana. AP.

Hukumar w w f tabukaci daukar kwararan matakai na kare hallttun dazuka. 1min 54sec.
Hukumar kula da kara halittu ta duniya WWF ta bukaci taron kare halittu da ya dauki matakai na kulawa dakuma kare halittun dake dazuka a duniya.

Maganar halittun dake dazuka itace babban abinda za afi maida hankali akai a taro na biya na kungiyoyi da sa ayi a Nairobi. Wannari kuwa shine zai biyo bayan taron kwamitin kwararu na kungiyar ta CBD wanda
akayi a Montreal cikin watan Janairu. Kwamitin kwararun tunda farko ya mika shirye-shiryen aiyukan sa na cewa dazuka sunyi rauni tilas a karfafa su. Rahoton sakatariyar ta lura matsayin yayi muni domin haka
akwai bukatar kara daukar mataki domin kawo karshen lamarin irin yadda ake asarar halittun dazuka mai
makon maida hankali kan daukar matasayi kan batun.

Hukumar ta WWF tace yayinda taron ya karfafa aiyuka da dama kara ya kirkiro shiruka masu kyau a rubuce, siadai ba a aiwatar da shirin ba a zahiri. Ya bukaci samun matakan da suka dace domin cigaba da
samun ingantaun dazuka. Haka kumaya cigaba da karfafa gwiwa samo hanyoyin aiwatar da shirukan da
aka amincewa na kula da dazuka. Haka kuma WWF na son kasashe su sanya hannu bisa yarjejeniyar daukar mataki wajen kare gandun

dazuka masu arzikin tsirrai da dabbobi daga barazana.
'Bawai maganganu da nazarce-nazarce-nazarce bane zasu dakatar da asarar dazuka d dabbobi' inji shugaban
shirin dazuka na hukumar ta WWF Jean-Paul Jeanrenaud. Saidai daukar mataki a zahiri kuma babu lokacin da yafi dacewa a dauka irin yanzu'.

WWF.
E-mail na barazana ga Amurka: 1min 32 secs.
Amurka na kara farkawa daga wata irin barazana kuma mai hatsari dake yaduwa ta cikin na'urar komputa. Dayawa daga cikin manyan kamfanoni sun bada rahoton cewar anobar ta fara samun su, wasu ma sun fara

rufe kamfanonin nasu. Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) tayi gargadin wasu da dama ma abin zai shafe su nan gaba kadan. 9
9 Page 10 11
July, 2000 (Hausa) CHANGE Radio
10
Tunda farko cikin watan nan miliyoyin komputa a duniya suka rufe saboda abinda suka kira 'Love bug' wanda ya samo asali daga kasar Filifines, wanda ya sanya akayi asarar dala miliyan dubu goma.
Sabuwar cutar komputa ana dauka ne cikin file daka tara da E-mail da akayiwa taken 'Resume-Janet Simons' sunan wani mai naman aiki. Sakon na neman masu daukar aiki da suyi cekin sunayen masu bada
kariya ga a mai namen aiki, wanda daukar aiki koda yana da irin wannan komputar in ya buda ba zai gani ba.
A halin yanzu dai hukumar ta FBI ta shawarci masu komputa kada su buda E-mail dake da kanun da ba
amince dashi ba. Yanzu haka dai an kauki matakai domin dakatar da wannan barazar tare da lalata shi baki daya.

BBC.
Kiwon lafiya mai kyau ko ina a duniya: 1min 59 secs.
Maganar kula da kiwon lafiya ingantace ga kowa da kowa shine za afi maida hankali akai yayinda kasashe 191 zasu hallara a taro na 53 na babban zauren taron kiwon lafiya na duniya a Genava.

Daga cikin manyan batutuwan da za afi maida hankali shine na kwayoyin HIV da cutar kanjamau wanda ke tauye aiyukan kwararu kan kiwon lafiyada Gwamuatoci a duniya. Daga cikin aukuwar cutar kashi 95
cikin 100 a duniya Afrika ce ke kan gaba inda mutane kimanin miliya 23 suka harbu da kwayoyin cutar. Haka ma zazabin cizon sauro ba abarta baya ba ganin cutar tana kashe miliyoyin mutane a duk shekara a
nahiyar ta Afrika. Haka kuma taron na lafiya zaiya tsokaci kan cutar kuturta da shan-inna dakuma tarin fuka.

Dr. Gro Harlem Brundtland babbar darektar hukumar lafiya ta duniya WHO cikin jawabi ta ga babban zauren taron ta baiyana wasu muhimman wurare hudu ga hukumar domin rage yawan mace-mace dakuma
nakasar jama'a tare da kasadar aiyukan larfiyar jama'a da rayuwar jama'a, tare da sanya lafiya gaba da tattalin arziki da cigaban kasa.

A hakikani ma kiwon lafiyar duniya yanzu bawai sai manyan jami'an kwararu kan kiwon lafiya ne ke tattaunawa ba, har ma da shugabanin Gwamnatoci ciki harda kungiyar nan ta kasashe 8 da suka cigaba a
duniya ta fuskar masana'antu watau G-8, inda suka tatauna kan. kiwon lafiya bayan na zuciyar Ministocin kudi yayinda suke halartar taron hukumar IMF da Bankin duniya yayinda suke tattaunawa game da rage
bashi.
A karo na farko cikin tarihi, kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya ya tabo maganar cutar kanjamau. Kiwon lafiya shine babban abinda kwamitin ya tattauna a rahoton sa, inda ya nuna irin tu'annatin da
kwayoyin HIV da cutar kanjamau ke yiwa al'umar duniya., wanda suka baiyana da cewar mummunar jafa'a'i ga tarinhin al'umar duniya cikin wannan sabon karni.
Neslink Africa.
Sabuwar yarjejeniyar da kasashen kungiyar acp/ eu sanyawa hannu. 2 mins 26secs. Zaa sanya hannu bisa wata sabuwr yarjejeniyar hadin kai na kungiyar EU/ ACP a Suva hadkwatar tsibiran
Fiji a ranar 6 ga watan Yuni 2000. Yarjejeniyar zata kara yaukaka dankon zumunci tsakanin kasashe 15 na
kungiyar kasashen Turai dakuma kasashe 71 na kasashen Afrika da Carrebeanian da Pacific watau ACP.

'Yarjejeniyar da akafi sani da yarjejeniyar Suve, zata maye wadda aka kulla a Lome da akafi sani da yarjejeniyar Lome, wanda kafin 'yan watanin baya ke wakiltan manyan batutuwa masu sarkakiya kan 10
10 Page 11 12
11
July, 2000 (Hausa) CHANGE Radio
kungiyar kasashen Arewaci da kudancin duniya. Saboda irin gagarumar nasarar da kasashen kungiyar ACP suka samu ta fuskar ciniki da harkokin kudi ne
ya sanya yarjejeniyar Lome tayi gaba ainun ta wajen samer da hadin kai ga kasashe mafi talauci. Misali kasashen Turai har yanzu suna la'akari da kasashe 71 dake kungiyar ta ACP ta wajen bude musu kofofin
kasuwanin Tural. Haka kuma yarjejeiyar Lome ta sanya Turai dafawa kasashen da suka jikata ta fuskar kudi na kungiyar ta ACP kamar faduwar dana kayan amfanin gona da sauran su.

Duk da haka wadan nan duk zasu zama tarihi da zarar an sanya hannu bisa yarjejeniyar suva, domin sabuwar yarjejeniyar bazatayi la'akari ba shi ba, daga shekara ta 2008 game da sassaucin kasuwanci.
Kafin wannan lokaci za akafa wata kungiyar yanki ta hadin gwiwar tattalin arziki (RIPA) kamar yadda yake kunshe cikin tsarin kungiyar ciniki ta duniya WTO. Domin hakan zai haramta duk wata yarjejeniya
irin ta Lome kuma nan gaba.
Yayinda yarjejeniyar na kintse domin saniya hannu, amma wurin da za ayi ba lafiya. A ranar 19 ga watan
Mayu ne akayi yunkurin juyin mulki a Fiji. Masu hangen abinda kaje-ya -zo sunyi imanin cewar wannan zaiyi kafar dandali na kaddamar da Afrika da Carebean da Pacific cikin kasuwancin duniya. Sakamakon

haka sai a sa ido tukuna. Newslink/ CFC.

Dandano jiran rabo.
Yarjejeniyar kyoto na cikin ajanda. 48 secs. Yanzu da shike sama da kasashe 80 ne suke sanya hannu bisa yarjejeniyar kyoto bisa kula da muhalli,
kungiyar Turai tana matsa lamba domin ta fara aiki a shekara 2002 wanda zai cike shekaru goma da taron kolin Rio. Saidai akwai manyan batutuwan da ba a fayyace ba tukuna sai taron gaba da za ayi a Hague
tsakanin 13-14 ga watan Nuwambar 2000. Taron baya na kungiyar anyi ne a Buenos Aires wanda ya ta'
allake wajen kammala dukkan wurare masu sarkakiya da ka' idojin aiki domin amincewa a taron Hugue. Wannan kuwa ya shirya filin domin samun biyan bukata a taro na gaba da za ayi.

The Courier.
Babban taron afrika kan amfani da albarkatun kasa: 44 secs.
Za agudabar da babban taron kan kula da amfani da albarkatun kasa a ougadougou kasar Burkina Faso tsakanin 24-28 ga watan Yuli 2000. Taron na baya irin sa an gudanar ne na hadin gwiwa tsakanin kungiyar

kula da halittu ta duniya Iucn da Asusun kula da labarkatun Afrika (ART), wanda kungiya ce mai zaman kanta a kudancin Afrika mai hadkwata a Zimbabwe da Afrika ta kudu.

Ministan kula da muhalli na kasar dake daukar bakwanci ne zai bude taron. An shirya taron ne domin ma'aikatan dake aiki a gandun dazuka da kula da albarkatu kasa. Haka kuma masu halartar taron akwai
jama'a masu sha'awa da hukumomin Gwamnata da kungiyoyi masu bada gudunmawa da kananan hukumomi.
The Courier.

Kyautar muhalli ga aikin kungiyar codeff a chile. 35 secs. Kyautar hukumar kare muhalli ta duniya UNEP ta shekara 1999 game da ceto yankuna da suka bushe an
baiwa wata kungiyar dake karkashin kungiyar Turai dake aiki a kasar Chile. Kwamitin (CODEFF) ne ke kula da wannan aiki wanda aka fara tun shekarar 1968 da wakilai 4,000. Aikin ya hada da kula da muhalli
da dabbobi da albarkatun kasa da gandun dazunka.
Aiki na daya daga cikin 25 da aka daga kungiyoyi sama da 100 a matsayin na gwaji domin kula da yankunan da suka bushe. 11
11 Page 12 13
July, 2000 (Hausa) CHANGE Radio
12
The Courier.
Jihar yobe zata kafa dokar haramta farauta da saran itauwa: 59secs. Jihar Yobe a Arewacin Najeriya kafa dokar haramta saran tatuwa da farauta dabbobin da ake ganin suna
cikin kasadar karewa baki daya a duniya daga watani shida na karshen wannan shekarar.
Yayinda dokar ta fara aiki, duk wanda ya karya ta za aci shi tarar naira 12,000 ko daurin watani shide ko a hada masa duka biyu. Wannan dokar ta biyo bayan la'akari da jihar tayi ne kan yadda ake saran itatuwa
domin yin girki, wanda ya yanyo talauci da matsalolin muhalli.
Matakin wannan jihar abin yabawa ne. Yayinda masana muhalli suna dubar hanyar fara aiwatar da dokar, samar da abubuwan girki ga jama'a mai dorewa domin maye gurbin itacen da suke girkin shine abin

marhabin domin taimatawa sabuwar dokar. The Guardian /CFC.

Fata na gari ga wanda ya tagaiyara: 1min. 42secs. Mutuncin mujalar Economist yafara shakku. Duk da haka irin yadda mujallar ke samun masu karanta ta
domin irin yadda take ruwaito abubuwan dake faruwa a Afrika, yanzu ya dauki sabon salo a mujallar da ta fito na 21 zuwa 25 ga watan Mayu. A shafin ta na farko mujallar ta buga hoton wani soja kato, wanda ya
rufe taswirar Afrika a bayan sa. Duk wannan abu bai isa ba sai mujallar ta cigaba da rubuta cewa' Nahiyar
Afrika bata da hango haske nan gaba'. Maimakon baiyana abinda mujallar ke kokarin fadi, sai ta rubuto wata wasikar da wani Mr. Chi Chi Okonjo ya rubuto daga Lagos Najeriya. Afrika na da matsaloli da

dama, wasu ita ta tajyowa kanta, amma bindigar da ake amfani da ita ba afrika ake kerawa ba. '
Irin yadda nahiya mai kasashe 54 take fuskantar matsaloli iri-iri abin takaici ne. Yayinda muke tabbatar da
karfi alkalami, wajan wayar da kan jama'a kan irin halin da Afrika ke ciki, muna rokon kamata yayi arika la'akari da irin abinda muke rubutawa.

Domin in har munyarda da abida mujalar ta Economist ta rubuta, ashe kenan babu dalilin fafutukar cigaban mu?.
Game da cewa Afrika itace koma bayan Nahiyoyi ba irin wannan jaridancin ne yakamata muyi ba kuma ba irin canjin da muke bukata ba kanan.
CFC.
Sashin Yara:

Najeriya zata karbi bakwancin taron yara kan yada labarai. 1min 40secs. Najariya zata karbi bakwancin taron kolin yankin Afrika na yara kan yada labarai daga 24-27 ga watan
mayu 2000 a Abuja. Taron shirye-shirye ne kan taro na uku na duniya irin sa da za'ayi cikin watan Maris a Girka a shekara ta 2001.

Wakilai daga Najariya da Togo da jumhuriyar Benin da Poland ne suka halarci taron. Hake kuma akwai 'yan jaridu da ma' aikatan rediyo da talabijin da manyan jami'an kafofin yada labarai da kungiyoyi masu
saman kanus, da kungiyoyin Gawamnati dakunma yara.
Daga cikin batutuwan da aka tattauna a taron sun hada da nuna shiruka masu tade handkali, da rashin
ingantatun shiruka da mutuwar shiruka irin na Afrika domin yara dakuma shishshighin na'urar Internet keyi cikin shirukan yara a Afrika. 12
12 Page 13 14
13
July, 2000 (Hausa) CHANGE Radio
Wata kungiyar yara da aka gaiyata a taron, ta baiyana ra'ayin ta a gun taron. Yaran bakin su yazo daya inda sukayi Tir da ta'addanci a shirukan rediyo da talabijin musamman irin na kasashen dake fama da
yake-yake as nahiyar. Haka kuma sunyi Tir da dillancin yara, da kaciyar da akeyiwa mata, da azabtar da yara da sanya su karuwanci dakuma nunawa mata bambanci.

Yaran sun bukaci da a kirkiro da tasoshin rediyo da talabijin na musamman domin yara a yankin Afrika tare kuma da sanya su yara gadan-gadan cikin shiryawa da gabatar da shirukan.
Taron ya kare ne da sanarwar bayan taro, inda ake kira ga samar da wani dandali inda yara da manyan
jami'an kafofin yada labarai na Gwamnati da iyaye zasu rika haduwa domin tattanawa yadda rawar su zata taimakawa domin amfanin yaran da sauran mutane ta kafofin yada ladbarai.

CFC.
Yadda agwagwan dawa ta sami farar da'ira a bayan ta: 1min31 secs.
Wata rana da dara cikin duhu ba farin-wata, Agwagawan dawa da 'ya'yan ta suna kiwon kusa da bukkar wani bakauye. Wannan Bakauyen dama yayi fentin bukkar sa da barar kasa, domin yana saran karbar

bakon dan uwan sa. Ya bar ragowar farar kasar cikin tukunyar da yayi aiki a waje.
Daya daga cikin 'ya'yan Agwagin nan cikin rashin sani sai ya tuntsurar da tukunyar farar kasar cikin duhu.
Sai wannan mutumi yaji ya farka yafito daga bukkar sa a fusace ya fara korar Agwagin yana fada. Agwagin sai kowa ya kama gaban sa yana gudu suka warwatse.

Cikin fushi, sai wannan Bakauyen ya dauki tukunyar fentin ya wurgawa Ita Agwagawar sai tukunyar ta fada bayan ta takuma makale sosai. Haken sai yazama mai amfani, domin fentin na haskaka bayan Agwagwar
yayinda take gudu, sai 'ya'yan ta suka ga hasken fenti suka fara dawowa suna binta da gudu har cikin dokar daji.
Yayinda Agwagwar ruwan taga amfanin farin fentin sai ta yanke. shawarar cewa kowanen su ya sanya farar fentin a bayan sa. Daga wannan lokaci har zuwa yau ake ganin farin abu a bayan Agwagwar ruwa.
When the hippo was hairy:

Lisenga da kwayaye: 1min 56secs. Lisenga na kan hanyar sa ta zuwa gari domin siada kwai cikin kwando. Saboda zafin rana kuma bai karya
kumallo ba kafin ya baro gida tun da safe. Bayan doguwar tafiya sai ya yanke shewarar hutawa gindin bishiya. Yayinda yake hutawa sai ya fara tunani kan irin kudin da zai samu bayan saida kwayayen.

In ya sayar Naira goma, to zaiyi amfani da kudin wajen sayo kaze. Yayinda kazar tayi kwai ta kwankwashe, 'ya'yan suka girma, sai ya saida su duka, kana ya sayo akuya.
In akuyar ta hayayyafa, sai ya sa wasu cikin garke, kana ya saida wasu, ya sayo sanuwa.
In ya sayo sanuwar sai ya jiya har lokacin da ta girma tayi gaho, gaho kuma manya, yazama mai arziki kenan.

Wannan mafarki nasa na azurta ya gaskanta a zuciyar sa, wanda yakai ga Lisenga yana dauki. Domin
wannan daukin ya fara rawa da tsalle, har akan haka ne ma ya buga kwandon kwayayen nasa da zai kai birni ya sayar, kwan kuma suka fashe duka.

Waiyo, Waiyo Lisenga ya fara kuka, ba zan sami arziki ba. Sai daga baya ya dawo cikin hankalin sa ya 13
13 Page 14 15
July, 2000 (Hausa) CHANGE Radio
14
shaidawa kansa cewa ka manta da wannan tunani naka na samun arziki.
Daga nan sai Lisenga ya juya zuwa gida, yace bai bukatar yin arziki ma. Abokan sa ma zasu rika zundan sa in har shine kadai a kauyen yayi arziki, domin haka yafi son cigaba da zama da abokan sa matalauta
maimakon yin arziki batare da su ba. Shangani folk tales.

Kan muhalli. Karin maganar da ba za a manta ba dasu: 1min 25 secs.
Hikimar afrika kamar haka: -Ba

kowani itace ne ke zama itacen girki ba a daji.
Karin Managar Sudan.

In kana son kasan yadda kasa take, tambayi kurege. Kan Hadin Kai.

Karfi sojin tururuwa ya dogara ne da yawan su. Karin Maganar Najeriya.
Kan adalci da zaman lafiya: Zaman lafiya na da tsada, amma yaci kudin sa.
Karin Maganar Kanya.
Domin kaucewa fushi, tilas ka faro daga farko. Karin Maganar Zambia.
Daga Littafin Karin Maganar Afrika.
Azabtar da dabba , tamkar kiyayya ga mahalicci ne. Cardinar John Henry Newman.

Ba zamu iya umurtan halittu ba sai munyi biyayya gare su.
Francis Bacon. Mawallafi 1561-1626

Allah Ya yiwa dan adam baiwar iya magana da kirkire-kirkire... amma babu abinda yayi sai lalata abubuwa.... dazuka sai reguwa sukeyi,
koguna na bushewa, dabbobin dawa na karewa, yanayi na gurbacewa duniyar kanta sai muni takeyi daga ainin siffar ta kowace dakika.
Anton Chekhov Dan wasan kwaikwayo na kasar Rasha 1860-1904.
Uncle Vanya (1900). 14
14 Page 15
15
July, 2000 (Hausa) CHANGE Radio 15

Page Navigation Panel

1 2 3 4 5 6 7 8 9
10 11 12 13 14 15

 

© 2002 Communicating for Change. All Rights Reserved
Developed by George Mbuagbaw