Go Back
Communicating for Change

Document Body Page Navigation Panel

Pages 1--13


Page 1 2
Vol. 11 No. 25 February, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
1
Aiyukan Raya Kasa
KIWON LAFIYA
Gwajin Tilas Kan Cutar Hiv Ga 'Yammata A Malawi 9mins. 12sec. 3
Shawarar da Coci ya yanke na gwada 'yammata kafin su sami dudin
tallafin karatu a Malawi ya janyo cecekuce.
.

Tallar kororon-roba ya cika batsa 7mins. 6sec. 5
Tashar Rediyon Gwamnatin Zambiya ta janye tallar amfani da
kororon-roba, saboda Gwamnati tace batsa tayi yawa a ciki.

MATA DA YARA.
Yawan yiwa yara fyade Sai Karuwa Yakeyi A Zimbabwe 10mins. 5sec. 6
Ana dada samun yiwa yara kanana fyade a kasar Zimbabwe, annobar
dake kara raba kawunan jama'ar kasar kuma babu mafita nan kusa.

Aikin Gona Da Abinci 5mins. 7
Yunwa na kara kunno kai yayinda kwari suka baiyana, kasar Tanzaniya bayan
da take kokarin farfadowa daga matsanciyar yunwar da tayi fama da ita.

Yanayin Muhalli
YANAYI
Akwai Alamun Samun Yanayi Mai Kyau Ga Kasar Kenya A Shekara Ta 2002 6mins. 6secs. 3
Za a hada Kenya da wasu sabbin hanyoyin sadarwa na tauraron dan adam a
badi, domin tabbatar da kulae da yanayi tare da yin gargadi cikin hanzari kan
duk wata jafa'i.

GURBACEWAR MUHALLI
Jihar Akwa-Ibom A Najeriya Zata Binciki Tsiyayar Mai. 3mins. 8secs. 4
Gwamnatin jihar Akwa-Ibom a Gabashin Najeriya ta kafa kwamiti kwararu
mai wakilai 12, domin ya binciki zargin tsiyayar Mai da akayi cikin watan
Nuwamba 2000.

Man-Inji Da Akayi Amfani Dashi Na Janyo Matsaloli A Birane 6mins. 7secs. 7
Rufe kamfanin mai na Biritania dake Zambia ya kai ga zubar d da man

inji dake barazana ga muhalli a Zambia.

HALITTU
Rakumai Sun Matsa Zuwa Tsaunukan Kenya 5mins. 4
An bukaci da a kauda daruruwan rakuman dake asunukan Kenya
domin kaucewar bala'i

Yankuna Masu Dausayi Na Duniya-Kamata Yayi A Gano Su 9mins. 10
Shekaru talatin bayan taron duniya kan yankuna masu dausayi, Ramser ya
tsaida 2 ga watan Febrairu a matsayin ranar yankuna masu dausayi na duniya.

An Sanya Gandun Dazukan Seychelle Cikin Taswirar Duniya 5mins. 5secs. 6
Kasancewa gandun daji na farko daga Afrika da ya baiyana a bukin baje
kolin duniya tsibirin Causin dake Seychelle ya sami shiga kan harkokin
dazuka a duniya.
1
1 Page 2 3
Vol. 11 No. 25 February, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
2
Ra'ayoyi
MATA
Kaidaito Kan Jinsi Gishirin Demokuradiya 17mins. 6secs. 8
Wata lauya a Zimbabwe Yvonne Malhunge tayi magana kan makomar
mata a demokuradiya tare da shigar su ainun cikin harkokin Gwamnati.

Abin La'akari
MATA
Tallafi Domin Fanm himta Ta Kwarai 6mins. 9
Wasu shahararun Mata marubuta sun sami kyautar yabo kan aiyukan su.

ABINCI
Jumhuriyar Demokuradiya Congo Ta Bullo Da Sabbin Irin Rogo 3mins. 5secs. 9
Cibiyar binciken aikin gona ta Congo ta bullo da sbbin irin rogo a
shekara 2000 wanda aka gwada a cibiyar kula da aikin gona na
yankuna masu zafi dake Ibdan Nigeria

Wa'adi
MAKAMASHI
Sabon Yunkuri Domin Samar Da Makamashi Mai Dorewa 4mins. 5secs. 10
A Wannan Karni
Kamar yadda babban darektan hukumar UNEP, Klaus Toepfer yace
kawayen tsirrai kan makamashi, irin su hasken rena da iska na daga
cikin manyan matsaloli da dan adam zai fuskanta cikin wannan karni.

Sashin Yara
MA-HARBI 17mins. 11
Jamina tana son zama maharbiya, amma da ta bata a daji, ta sami
sabbin kawaye wadanda suka sanya ta canja ra-ayin ta kuma da yadda
take daukar duniya.

Dandano Jiran Rabo
Ga wasu karin maganar da ba za ka manta ba a bukin nahiyar Afrika. 12 2
2 Page 3 4
Vol. 11 No. 25 February, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
3
Labarai
Gwajin Tilas Ga Yammatan Malawi Na Makarantu. 9mins. 12secs. Babban Cocin kasar Malawi ta yanke shawarar yiwa duk wata Yarinyar dake son samun kudin
tallafin karatu, gwajin ko tana dauke da kwayoyin cutar HIV. Cocin mai suna Church of Central African Presbystarian (CCAP) yace duk wanda ke son samun kudin tallafin karatu daga Cocin,
wanda ya hada da kudin karatu da na kwanan dalibai da saurat kayan makara tilas ne sai anyi mata gwaji kan ko tana dauke da kwayoyin cutar HIV.

Hukumomin Cocin sun kara da cewar, tilas ne wadanda suka ci gwajin, za a tura su makarant Sakandare ta Neno dake bakin iyakar gundumar Mwanza. Wadanda kuma suke dauke da kwayoy
cutar koda aji newa suke nan take za a dakatar da tallafin da ake basu. In har suna bukatar cigaba da karantun su tillas sune zasu dauki nauyi biyan kudaden karatun su.

Shirin kula da cutar Kanjamau na kasa (NACP) ya baiyana wannan ynkuri na Coci da cewar nuna bambanci ne karara. Darektan shirin Dr. Owen Kalua ya shaidawa manema labbara cewa, manugar
Gwamnati ne cewa babu wanda za a nunawa bambanci saboda kawai yana dauke da kwayoyin cutar HIV. Hakan yace babu abinda zai haifar illa dkile wadanda ke dauke da kwayoyin cutar. Amma Rev.
Daniel Gunya babban sakataren Cocin CCAP, ya tsaya kai da fata cewa tilas ne sai anyi gwaji ga masu bukatar samun kudin tallafin, kuma wannan ba wai nuna bambanci bane. Domin wadanda basa
son a gwada su sai su cigaba da biyann kudin karatun su, domin haka babu bambanci inji shi. Amma
Klaus na NACP yace Cocin ya maida batun kudin da gwajin cutar HIV wanda hakan bai dace ba ko kadan. Yace irin 'yammatan da suka kamu da cutar ta hanyar yi musu fyade ko karin jini, zasu shiga

cikin tasku ba bisa laifin su ba.
Shi kuwa Charles Gunsary , darektan makaratanr Sakandare da ilmi mai zurfi dake ma'aikatar ilmi,
kimiya da fasaha, yace ma'aikatar tayi mamaki kan matsayin da Cocin ya dauka. 'Munyi mamaki, domin mu a Malawi ba wanda ya taba daukar cutar HIV a matsay ma auni kan daukar aiki' inji shi.

Amma ma'aikatar wanda aikin ta ne sa ido kawai zata iya shawar tar Cocin ne kadai. Ba zasu iya tilas ta masa ya canja shawarar sa ba.

Rev. Gunya yace lallai yana mai mamakin matsayin Cocin, akana wata kila yana kokari ne na tabbatar da masayin sa na yaki da mugunyar cutar ta kanjamau. Yace koda shike wannan wata hanya ce guda,
shugabanin Cocin suna iya tsarkake Yammata daga saduwa da. Maza wanda ta haka zasu kaucewa kamuwa da cutar. Haka kuma shirin bada gudunmawar jini da akeyi shekara-shekara zai dakishe
karakainar da 'yammata keyi, kana ya basu wata hanya ta kaucewa kamuwa da mugunyar cutar dake
kisa inji shi.

Malawi na daya daga cikin kasashen dake sahun gaba da cutar kanjamau la tayi kamari a duniya. Kamar yadda kididdigar baya-bayan nan ta nuna daga hukumar kula da kare cutar kashi 14 cikin dari
na al'umar Malawi Miliyan goma ne ke dauke da cutar kanjamau.
Kyakkyawan Yanayi Ga Kenya A Shekara Ta 2002 6mins. 6secs. Za a sada Kenya da hanyar zamani ta tauraron dan adam cikin shekara mai zuwa. Sabuwar hanyar da
zata hade kasashe 45 masu tasowa, za a kaddamar da ita ne a tsibirin Guyana dake farfajiya tekun Afrika ta yamma. Ana saran zata tabbatar da ingancin hange yanayi tare da kyautata tsarin yin
gargadi yayinda aka hango jafa'i. 'Muna iya baiwa abokan huldar mu labarin ingantace, domin inganta 3
3 Page 4 5
Vol. 11 No. 25 February, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
4
bukatun su' inji Ayub Shaka mukadashin mataimakin darektan kula da yanayi. Da yake jawabi ga
kasa a ofishin sa, Mr. Shaka yace sabuwar hanyar zata bada kididdiga kan yanayi har sau biyu, wanda zaiyiwa kasashen Turai da na Afrika aiki, zai kuma rika samar da bayanai a duk bayan mintoci 15,

bawai ko wani bayan rabin sa'a ba kamar yadda yake yanzu.
Ma'aikatar kula da yanayi ta Kenya ce zata rika kula da shirin rukunin aikin a Afrika da Caribean
dakum Pacific. Kamar yadda Mr. Shaka ya fadi, kungiyar Turai ta amince da samar da kudin da kasashen zasu sami sukunin inganta tasoshin tauraron su na dan adam.

Kenya zata kafa sabuwar tashar tauraron dan adam din ta, wanda zata rika karbar sakwani tare da inganta tasoshin tara bayanai guda 35 a sassa daban-daban na kasar domin tafiya daidai da zamani.
Haka kuma aikin zai horas da jami'an kimiya wani bangare na shirin dake gudana cikin shekaru uku. Cibiyar auna fari ta Kenya wanda ke aiki tare da IGAD, ita ma zata ci moriyar wannan shirin. Kamar
yadda kungiyar Turai tayi bayani sabuwar hanyar ana saran zata samar da akalla tsarin labarai ninki 20 kan yadda ake samarwa yanzu. HJaka kuma zata samar da layuka 12 na tara bayansi mai makon
uku da ake dashi yanzu, zai kuma rika yada abubuwan dake faruwa na gida cikin nagarta.
Hukumar kula da yanayi ta Turai tace, bayanan da za arika tarawa za ayi amfani dasu ne wajen karfafa kula da karfin iska dakuma kariya ga harkar sufurin jiragen ruwa.

Sabuwar hanyar tauraron dan adam din ana saran zata fara aiki ka'in da na'in cikin shekara ta 2002,
wanda a karo na farko zata bada gudunmawa kan sa ido wajen kula da yanayin muhalli irin su kwararowar hamada da canjin yanayi dakuma wutar daji.

The Nation:

Jihar Akwa-Ibom A Najeriya Na Bincikar Tsiyayar Mai 3mins. 8secs. Gzamnatin jihar Akwa-Ibom dake Gabashin Najeriya ta kafa kwamiitin kwararu mai wakilai 12
karkashin shugabancin Farfesa Etie Akpan, wani masani kan harkar jiragen ruwa, domin ya binciki
zargin da akeyi cikin watan Nuwambar 2000 na tsiyayar mai a jihar. Kwamishinan kula da muhalli Obong Isidore Akwan-Ebe ya shaidawa 'yan jaridu cewa rahotanin dake isowa ma'aikatar sa, sun

nuna cewa an sami mummunar tsiyayar mai a jihar.
Yace an baiwa kwamitin mako 6 da ya mika rahoton sa ga Gwamnati, bugu da kari kwamittin zaiyi
aiki da bayanan da aka samu ta tasoshin tauraron dan adam da aka kakkafa su a muhimman wuraren kula da muhalli na jihar Akwa-Ibom inji shi.

Cikin watan Nuwamban bara ne kamfanonin Exxon/ Mobil bayan da suka kewaya da manema a ruwayen tekun suka ki yarda kan cewar an sami tsiyayar mai a jihar. Kwamishinan wande ya baiyana
kamfanonin na Exxon/ Mobil da Elf da Shell wadanda sune manyan kamfanoni uku dake harkar mai a jihar ta Akwa-Ibom, kwamitin kwararun zai baiyana hakikanin gaskiyar zargin kan ko wa ke d a
kayan da aka ce suna tsiyayar da man. Akpan-Ebe Obong ya baiwa jama'a tabbaci cewar nan gaba kadan kwamitin na Farfesa Etie Ben zai kammala aikin sa kuma za a baiyanawa jama'a irin abinda ya
bankado.
Rakumai Sun Matsa Daga Tsaunukan Kenya 5mins. Jami'in kula da zurga-zurgan yankuna masu tsirrai, Farfesa Wangari Maathani yayi kiran da a kauda
daruruwan Rakuman dake tsaunukan kurmin Kenya. Farfesa Maathani ya rubutawa shugaban ma'aikata, Dr. Richard Leakey, inda yake bukatar daukar mataki kan wannan batu. Yace dabbobin 4
4 Page 5 6
Vol. 11 No. 25 February, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
5
zasu iya lalata kyakkyawan yanayin tsaunukan, wanda yake da ruwa tilas ne a kare yankin ko ta halin
kaka. Zurga-zurgan dabbobin na Kenya zuwa wannan kurmi ya nuna a zayhiri irin yadda kwararowar hamada ke tsanani, Rakum dai dabbobi ne na Hamada inji shi.

Tsananin yunwa da karancin abinci dai ya kusan zama jiki a Kenya muddin ba ayi wani abu domin kare dazuka ba, domin samun ruwan sama, wanda ke tallafawa aikin gona ainun. Yana ko magana ne
kan rahotanin da jaridu suka buga masu kiwo na korar daruruwan Rakuma zuwa sashin Gathiuru na tsaunukan Kenya domin samun abinci, haka wani wakilin majalisar kasar D. r Chris Murunguru yayi
irin wannan korafi, inda a mazabar sa ne yankin na Gathiuru yake. Amma Gwamnati tayi sauri wajen maida martani, inda tace tana sa ido ainun kan zurga-zurgan masu kiwon. Wani jami'in' yan sanda
Elijah Shamalla ya ziyarci aynkin domin tantance halin tsaro a sakamakon rahotanin da aka bayar kan akwai yiwuwar fito-na-fito tsakanin makiyayan da manoma dake zaune a bakin kurmin.

Farfesa Mathina yakai maganar da kwamishinan gundumar Omar Sallat, na cewar makiyayan suna tafiya ne da dabbobi bisa tilas domin ceton dabbobin su. Ba asamu ruwan sama ba kuma babu
amfanin gona saboda lalata dazukan da akeyi, jama'ar Kenya suna fama da yunwa' inji Farfesu Maathini.
The Nation
Tallar Kororon Roba Ya Cika Da Batsa 7mins. 6secs. Yakin da aka daura kan cutar kanjamau da kwayoyin HIV a kasar Zambia yakai wani matsayi yayinda

aka janye taller yin amfani da kororon roba ta gidan rediyon kasar, saboda Gwamnat tace akwai batsa ainun cikin tallar,. Shugabanin Coci daga majalisar kiristocin kasar tayin kamun kafa ainun,
wajen ganin an janye wannan tallar daga gidajen rediyo, wanda kungiya yaki da mugunyar cutar ke
gudanarwa cikin 'yan watanin nan ta gidan rediyon zambia (ZNBC) wanda yake kwadaitawa matasa yin alfasha.

Ita kan ta gwamnati ta raba hankalin ta biyu kan wannan batu. Ministan lafiya Enock Kavindele ya roki shugabanin kiristoci kwanakin baya da su fuskanci gaskiya kan yadda cutar kanjamau ke illa,
saidai kuma Ministan ilmi Godfrey Miyanda ya goyi bayar shugabanin kiristocin. Shugaba Frederick Chiluba, wanda a shekarar 1991 ya maida kasar mai bin tafarkin kiristanci, ya fadi cewa, tallar
amfani da kororon roba wata alama ce ta rashin da'a. Shawarar da gidan rediyon kasar ya tsaida ZNBC na janye tallar amfani ka koron roba domin biyan bukatun jama'a, kungiyoyin yaki da mugunya
cutar sun caccaki tsarin. Jami'n kula da yaki da cutar na kasar Masauso Nzima yace wata kila dai mutane basu da cikakiyar masaniya kan irin tu'annatin da cutar keyi. Kororon-roba na daya daga
cikin manyan hanyoyin dakile yaduwar cutar kanjamau domin haka bai kamata ayi watsi da tallar
hakan nan ba batare da samar da wata hanyar da za a bi ba.

An kiyasta akwai 'yan kasar Zambia kashi 20 cikin dari magidanta dake dauke da kwayoyin cutar HIV. Kamar yadda gwamnati tayi bayani sama da mutane dubu dari 7 ne suka mutu daga wannan

mugunyar cutar tun cikin shekarun 1980, kana sama da yara dubu dari 650 ne zuka zama marayu. Yanzu haka yara tsakanin dubu 25 zuwa dubu 30 ne ke dauke da kwayoyin cutar ta HIV, yayinda
yara bakwai daga cikin kowasu yara 10 ne ake kyautata zato bazasu kai shekara biyar a duniya ba.
Da yake baiyana kan yadda al'ada ta rashin amincewa kan tattaunawa kan batun jima'i a baiyanar
jama'a, Nzima yace yayi imani koken da akeyi na kororon-roba kan yadda ake tallar a daidai lokacin da mafiyawan jama'a ke sauraro, lokacin da iyaye ke cin abincin dare tare da 'ya' yan su.

Koda shike lokacin bai dace ba, amma duk da haka akwai abinda ake kira tarbiya daga iyaye. Coci na bukatar da asamo wata sabuwar dabara domin yaki da mugunyar cutar. 5
5 Page 6 7
Vol. 11 No. 25 February, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
6
Nils Gade babban jami'in kungiyar kula da lafiyar iyali ta Zambia yace shirin yaki da kanjamau na majalisar dinkin duniya ya amince da amfani da kororon-roba kan hanya mafi inganci domin kare
kamuwa da cutar kanjamau . . . musamman ga 'yan Zambia, wadanda basu san matsayin su ba ko suna dauke da cutar ko a'a, intergrated regional.

Ana Dada Samun Karuwar Yiwa Yara Kanana Fyade A Zimbabwe 10mins. 5secs. Kimanin kararrakin yiwa yara fyade da shekarun su yakama daga watani uku dubu biyu ne aka
gabatar a kotuna bara a Zimbabwe. Mahukunta da sauran Babban abindamuwa ga mahukunta da kungiyoyin mata shine kan yadda wannan miyagun aiki ke karuwa tsakanin jama'ar da bokaye ke
basu shawarar suyiwa yara fyade, domin warkar da cutar da suke fama da ita wanda taki jin magani.
Imanin da masu aikata fyade sukeyi ne cewar bokaye sunce musu saduwa da Yara kanana zai warkar da cutar su wasu kuma sunyi imanin cewar aikata irin wannan laifin yana kawo sa'a ga jama'a.

Sakamakon irin wannan tu'annati bashi da kyau tsakanin wadanda akayiwa da iyayen su. Akasarin yaran da akeyiwa fyaden suna kamuwa ne da cutuka irin su tunjere da ciwon sanyi har ma da cutar
kanjamau. Kididdiga ya nuna kashi 70 cikin dari na yaran da akayi wa fyade a Zimbabwe suke kamuwa da irin wadan nan cutuka. Kiyasi ya nuna cewa mutane dari biyar da ke kamuwa da cutukan
mata kowani mako, kashi 30 cikin dari duk yara ne wadanda ke fadwa hannu masu yi musu fyad. Jinkirin da ake samu na gano lokacin da aka aikata laifin yakan sanya su su kamu da irin wadan nan
cutukan. Wata kungiyar matsin lamba, da kungiyar kare yara sunce ana gano irin wannan barna ne
bayan shekara guda. Wani nazarin kuma ya nuna cewa yiwa yara fyade sai karuwa yakeyi kamar wutar daji a kasar akasarin 'yammatan basu wuce' yan shekara takwas, wanda shine rabin shekarun

da yarinya zatayi kafin ta san maza. Hukumar bincike da shugaba Rober Mugabe ya kafa shekaru biyu baya, ya gano cewar kusan akasarin yara suna fama da barazanar yi musu fyade, kana ya bada
shawarar kafa doka mai tsanani domin kare yaran. Irin wannan cigaba yanba nuna damuwa saboda
hatsarin da yaran ke fuskanta domin kamuwa da cutukan Mata da kwayoyin cutar HIV da kanjamau inji hukumar.

Har yanzu kasar bata da tabbas, duk a nazarin da akayi kan yiwa yara fyade da dalilan dake janyo haka, wanda ke faruwa har can yankunan karkaran kasar. Yayinda kararda kotuna ke sauraro ya sany
yawan aikata laifin kan shawarar da bokaye ke bayarwa mai makon yadda al'adun zamani ke gurbata zamantakewa.

Kungiyoyin Mata sunce laifin na karuwa ne saboda hukuncin da kotuna ke yankewa masu irin wannan laifin da tsauri.
Gandun Dajin Seychelle Wajen Bukin Baje Kolin Duniya 5mins. 5secs. Tsaibirin causi dake kasar Seychelle ya sami karbuwa a duniya ta fuskar yawon bude ido dakuma
kulawa kan yankunnan bakin teku, bayan da a karon farko wani yanki na Afrika ya shiga cikin bukin baje kolin gandun dazukan duniya na shekara. Rahotani daga tashar jiragen ruwa ta Louis sunce
Taibirin Causin shine samfur mafi kyau kan harkar yawon bude ido dakuma kula da aiyukan sufurin jiragen ruwa cikin mujallu biyu da suka fito na baya daga kungiyoyin duniya.

Sashin na musamman dake kan kulawar Birdlife na Seychelle kuma shine samfur kadai cikin littafi
'domin kyautata harkar yawon bude ido a sashin gabasin Afrika dakuma tekun India. Cikin wasikar da aka aikawa Ministan kula da harkokin zurgazurgan jiragen sama Simone de Comarmond, babban

sakataren kungiyar cinikayya ta duniya Fransco Frangilli yace na tabbatar yana da ingancin harkokin sufurin jirager ruwa a Seychelle. Littafi na biyu-kan jiragen ruwa dakuma kariya' jagora ga masu 6
6 Page 7 8
Vol. 11 No. 25 February, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
7
tsarawa dakuma kulawa, wanda kungiyar kula da halittu ta duniya. Taibirin Causin ya baiyana a
wasy fanoni biyu na sabon littafin. Na farko shine wanda ya hada kan aiyukan gudananrwa na sibirin, wanda akayiwa lakani 'Tsibirin Causin-Teku da halita da kungiyoyi masu zaman kansu ke kulawa'.

Ya baiyana bincike da sa ido da ilmantar wa dakuma nasarorin mulki.
Niemal Jian Shah babban jami'in BirdLife Seychelle cewa yayi nasarar tsibirin ta shafi daukacin
yankin kuma kamata yayi ta zama abin alfahari ga shirin baki daya. 'Mutane suna da ra' ayoyi daban-daban, saidai kuma abin baki daya ya dogara kan yadda aka sami nasarar sanin tsibirin a duniya baki

daya' inji Shah. ' Ba zamu sassauta ba kan wannan nasara saidai zamu daura damara domin karin samun wasu nasarorin a tsibirin na Causin ' \yakara da cewa.
allafrica. com

Gurbatacen Man Inji Ya Janyo Matsaloli A Birane 6mins. 7secs.
Gurbatacen man inji na barazana ga muhalli a Zambia a kamfanin mai na Biritania dake Zambia, wanda ada shike sayen irin wannan gurbatacen man, domin sarrafawa a masana' antar dake tsakiya

birnin Kitwe da ake hako bakin karfe. Amma saboda rufe masana'antar dakuma daina gyara motoci yanzu an fara zubar da gurbatacen man wande ke kokarin gurbata ruwan da jama'a sha.

Gurbatacen man inji abune da yakamata a nuna damuwa kanta ganin yadda take illa ga tsirrai da ruwa dakuma yanayin muhalli baki daya ciki har da iskar da ake shaka inji Jewitt Masinja, babban
sakatare a ma'aikatar kula da muhalli da albarkatun kasa.
Saboda haka ne cibiyar kula da datti ta kasar Zambia cikin 'yan kwanakin nan tayi taro karawa juna
sani, inda aka tattauna kan gurbatacen man injin. Daga cikin wadanda suka halarci taron harda masu gyara motoci da kamfanonin dake saida man injin. Babban dalilin yin taron shine gyara wuraren

gyaran mtoci da aka rufe dakuma tasoshin saida mai.
Bayan rufe kamfanin mai na BP dake Kitwe a Zambia dakuma rassan sa dake Zimbabwe da tasoshin
gyaran motoci dana saida mai, sai aka rika samun tsiyayar gurbatacen mai zuwa magudanun ruwa. Wasu lokutan irin wannan man, yana kwarara har wuraren da ruwan sha ke da koramu wani lokacin

har gonaki dakuma gidajen mutane dake kusa da yankin. A sakamakon haka sai ruwan da jama'a da dabbobi ke amfani dashi ya gurbace kifaye su mutu kana sauro su sami wuraren kiwo.

Yanza cibiyar na hada karfi da sauran rassan dake Afrika ta kudu da Namibia da Zimbabwe dakuma Botswana danufin samo wata dabara ta yadda za arika sarrafawa irin wannan mai gurbatace. Ana
fata za asamo sahihiyar hanya ta yadda za arika kulawa da wannan mai yadda yakamata. PanAfrica news Agency

Yunwa Ta Fara Kunno Kai Yayinda Tsutsotsi Suka Fara Bulla 5mins. Yayinda Tanzania ta fara farfadowa daga mummunar karancin abinci da tayi fama dashi kasar na
kuma fuskantar hatsarin yunwa saboda bullar tsutsa masu lalata kayan gona. Gwamnati ta bada sanarwar cewa biyar daga cikin yankuna ashirin dake gundarin kasar Tanzania tuni wadan nan tsutsoisin
sun baiyana, kana wasy gundumomin shida suma suna fuskantar wannan barazanar. Gundumomi
biyar da suka kamu da tsutsotsin sune Dodoma da Arusha da Mbeya da Iringa dakuma Singida, inda aka ruwito tsutsotsin sai kara yawaita sukey mai tsoratarwa. Uku daga cikin gundumomin, Arusha

da Kilimanjaro da Tanga kade iyaka da Kenya ta Arewa ana fargabar suna iya ketarawa har cikin kasar ta Kenya daga gundumar Mbeya har zuwa sauran makwaitan kasashe Malawi da Zambia. 7
7 Page 8 9
Vol. 11 No. 25 February, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
8
Koda shike ma'aikatar aikin gona da abinci batayi bayani kan irin ta'adin da tsutsotsin sukayi ba saidai ana kiyasin cewar dubban daruruwan tan na hatsi ne suka salwanta a fili mai fadin kadada
dubu 7 da dari 7 da 80 a gundumomin biyar. Gwamnatin Tanzania tana shiri mika kokon baran ta ga hukumar abinci da aikin gona ta majailisar dinkin duniya dake birnin Roma danufin samun dala
miliyan daya na yakar wadan nan tsutsotsin. Haka kuma Tanzania tana fuskantar barazanar farin
dange da tsuntsaye jan baki, wanda gwamnati tace suna kara barazanar karancin abinci muddin ba wani mataki aka dauka ba.

Wani jami'i a sashin kare amfanin gona Mr. Sergei Mutahiwa ya gargadi kasashen dake makwabta da Tanzania da su kwana da shirin dakile gurgusowar tsutsotsin.
the east africa.

Ra'ayoyi
Daidaiton Jinsi Gishirin Demokuradiya 17mins. 6secs. Nuna bambanci a wajen zabe ya zama ruwan dare a zabukan da akeyi a Zimbabwe tun 1985, kan
haka saben da akayi na wakilan majalisar dokokin kasar a bara mutane suka fito ainun domin kada
kuri'a. Bayan zaben 1980 irin wannan tagaja-tagajan zabe ya samu gindin zama. Domin haka ne mutane suke gani babu wata bukatar su fito suyi zabe. Mata a wani bangare masu jefa kuri'a suma

suka bi sahun hakan. Yawan mata fiye da maza shine ya sanya suka zama gishirir kan duk yawan wakilan da zasu shiga majalisa ta hanyar zabe. Saidai kuma ana daukar Matan da gaske kan harkar
zabe? Ko ana sanya su zama mawaka a wajen taron siyasa kawi domin maza? Zasu cigaba da zama
haka ke nan na masu yiwa maza waka a yakin neman zabe suna masu durkuso a dandamalin filin jirigin saman Harare domin ladabi ga mazan wasy matan? Lallai lokaci yayi da mata zasu kasance

sahun gaba wajen masu nada kuk wanda suke so, kuma kamata yayi su zama masu tsayawa zabe.
A matsayin su na masu zabe yanzu kamata yayi mata su kara jan damara, domin yin nazari agame
rawar da suke takawa kan harkar siyasa. Domin haka yazama wajibi wawan dadewar jam'iya haka kuma yawan lokacin da yayi na yin watsi da mata ko rashin basu fifiko kan yakin zabe.

Bebbar illar dake Zimbabwe itace in duk matan Zimbabwe sunkai minzilin yin zabe, kuma suka taru suka zabi jam'iya guda, wannan jam'iya bata bukatar kuri'ar kowani Namiji domin samun rinjaye
cikin majalisar dokokin kasar. Hakan ya nuna babu dokar tsarin mulki na Gwamnati ta nada maza zalla har 30 cikin majalisa. Abin bakin ciki a Zimbabwe shine yadda tsarin jam'iyu suke ta yadda
babu yada mata zasu taka rawar azo agani kamar yadda maza keyi a tsarin siyasar kasar.
Muddin ba jam'iya tana da madogaro wajen samun kudi ba bisa doka, wanna jam'iya ba zata iya
samun kudaden tafiyr da aiyukan ta. Koda jam'iya tna da kudi bawai shike nan zata tsaida 'yar takara mace ba kai tsaye. Saboda haka ne yakamata Mata su sake tsarin kan su cikin jam'iyun siyasa.

Gwamnatin da take da kudurin samar da yanayi mai kyau domin daidaiton jinsi dkuma mulkin adalci bisa tafarkin demokuradiya shine giahirin demokuradiya. Inhar domin tashin tsaye wajen shiga takarar
shugabancin kasar. Kamata yayi Gwamnati ta dauki nauyi inganta daidaiton jinsi, wanda zata rika jaddada muhimmancin maza da mata bisa al'umar kade bin tafarkin demokuradiya.
Abridged opinion of Yvonne Malhunge, in the Zimbabwe Independent 8
8 Page 9 10
Vol. 11 No. 25 February, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
9
La'akari
Al'umar Mu Fa! Kyautar Fahimta 6mins. Wasu mata hudu marubuta sun fami kyautuka na farko na littafi mai suna' Our people oh. domin
fahimta'. An sami kudin da ake bayarwa kyautan ne daga kudin cinikin wani littafin da wata shaharariyar 'yar jarida' yar kasar India, Alka Raza matar tsohon jakadan Amurka a Najeriya, Susan
Twadell, domin bukin shekarar tsoffi ta majalisar dinkin duniya. Yayi tsokaci kan tarihin rayuwar wasu mutanen da suka manyan ta a sassa daban daban na Najeriya daga tsoffin 'yan jaridu zuwa
makada. A matsayin babban bako, darektan gunduma na gidauniyar Ford, Dr. Akwasi Aidoo kyautar wata gada ce tsakanin matasa da tsoffi 'yan Najeriya, wanda ya shige shalholiya, da wadanda sukayi
fice dakuma mata masu kamar maza marubuta wadanda ke da sha'awa wajen bada labarai kan
Najeriya gidauniyar Ford ce ta bada kudin somin tabi.

Daniele Landry wakilin hukumar kula da yawan jama'a ta majalisar kinkin duniya da yake baiyana ra'ayin sa manyan bakin duniya suna iya zama masu tsokaci dakuma la'akari kan abinda ke gudana
a kasar da suke bakwanci fiye da 'yan kasar. Wata sa'aa mutum na neman abinda zai wallafa wanda
babu gishiri cikin sa game da mutanen kasar da yakeyiwa aiki.... Littafin ya nuna irin yadda mutumin da ba kowa ba zaiyi fice a ryuwa a Najeria. '

An bada tabbaci wajen zaben wadanda suka sami kyautar daga yankunan kasar daban-daba Nneka Osakwe malama a jami'ar Nnamdi Azikiwe dake Awka, wanda ta sami kyautuka iri-ira ciki da
wajen Najeriya kan harkar ilmi kuma 'yar rajin kare hakkin yara, da wata marubuciyar salon magana da tatsuniyoyi Binta Muhammed daga sashin Arewacin kasar.

Haka kuma akwai Flowrence Inokweje an zabo ta daga yankin tsakiyar Arewa bisa aikin ta na wasan kwaikwayo mai kuma rajin kare matasa. Sai Mrs. Kemi Wale Olaitan wata ma'aikaciyar Rediyo
daga sashin yammacin kasar, wanda tayi tsayin daka wajen kare matan Afrika, Kowace ta sami kudi naira dubu dari, domin tallafawa kokarin ta na inganta tattalin arziki da zamantakewa.
CFC

Jumhuriyar Demokuradiyar Congo Ta Bullo Da Sabbin Irin Rogo 3mins. 5secs.
Cibiyar kula da aikin gona da bincike ta jumhuriyar demokuradiyar Congo ta bullo da wasu irin rogo har 200, wadanda akayi gwajin su a cibiyar nazarin tsirrai na yankuna masu zafi dake Ibadan najeriya.

Anasaran irin zasu karbi yankunan da za a rarraba su ga manoma dake karkara. Cibiyar tace bisa haka ne aka fara yin gwaji a wasu yankuna biyu dake bayan garin birnin Kinshasa watau Mvawazi da
Mbakana. Cibiyar gwajin farko an kafa ta ne tareda taimakon babbar cibiyar yayinda na biyun na
samun goyon bayan cibiyar raya tsirrai ta Mbakana, inda aka shuka iri har guda dubu dari. Bullowa dakuma gwajin wadan nan irin na daga kokarin da Gwamnatin Congo keyi ne na kauda cutar dake

addabar rogo.
Rogo dai shine babban abincin sama da kashi 70 cikin dari na al'umar Congo musaman a lardunan
Bundundu da gangaren Congo dakuma birnin Kinshasa. Wannan kokarin dake samun goyon bayan hukumar kula da abinci da aikin gona ta majalisar dinkin duniya na daga yunkurin da akeyi na inganta

harkar wadata abinci. PanAfrican News Agency 9
9 Page 10 11
Vol. 11 No. 25 February, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
10
Wa'adi
Zabura, Tabbatar Da Makamashi Babban Aiki A Sabuwar Karni 4mins. 5secs. Abokan halittu wajen samar da kamamashi, irin hasken rana, da iska na daya daga cikin muhimman
batutwa dake fuskantar dan adam a wannan karni. Babban darektan UNEP Mr. Klaus Toepfer ya shaidawa taron zaburar da shirin makamashi a Paris cewar tilas ne a sanya batun cikin gundarin
rayawa dakuma fuskantar barazana kan canjin yanayi da bukatar magance talauci da rashin lafiya a kasashe masu tasowa'., inji Toepfer. Tabbatar da zaburar makamashi da rashin cutar yara na nufin
tabbatar da cigaba da aiyukan birane dakuma kasancewar su wurren da za a zauna ayi kuma aiki
domin tabbatar da ganin mafiya talauci a duniya ba a tilas ta mus sare dazuka dake cike da halittu domin yin girki ba ko dumama jikin su' inji.

Ra'ayoyin ne aka gabatar cikin watan Janairu a taron kwamitin sha yanzu magani yanzu na kungiyar G-8 kan samar da makamashi, inda Ministoci daga kasashen Afrika 10 a hedkwatar UNEP dake
Nairobi suka daidaita kan amfani da makamashi. Ministocin zasu mika bayan su a taro na tara na hukumar raya makamashi da za ayi cikin watan Afrilu. Harsashen na Toepfer yazo ne daidai lokacin
taro na 2 na majalisar gudanarwar inda Ministoci zasu tattauna daga ranar 5 zuwa 9 ga Fabrairu a Nairobi kan zaburarwa dakuma cigaban makamashi.
PanAfrican News Agency

Yankuna Masu Dausayi, Duniyar Da Yakamata A Samu 9mins. Wakilan farko wadanda suka kokarta daga kasashe 18 a karamin garin nan Ramsar dake kasar Iran
dake gabar tekun Caspain a karshen watan Janairu, tilas ne su yi alfahari kan irin nasarorin da suka samu a lokacin. Taron na yankuna masu dausayi an kammala shi ne ranar 2 ga watan Fabrairu. Yau
shekaru 30 daga bisani yarjejeniyar ta zama wani jigo da wasu bangarori 123, domin tabbatar da yin amfani da yankuna masu dausayi. Wadan nan shafuka kalilan dake cikin yarjejeniyar Ramser, wadanda
sukayi kokarin kirkiro tsarin kulawa tare da kare barazana ga duniya.
Shekarun baya sun nuna cewar yarjejeniyar kan yankuna masu dausayi ya shige jigo kan dokar kasa
da kasa, wanda za a ami kasashen da zasu basu goyon baya, al'umar dake da ilmin kimiya da sauran kungiyoyin kasa da kasa da kungiyoyi masu zaman kan su da sauran sassan zartaswa. Bisa haka ne

taron na yankuna masu dausayi suka dogara kan batutuwan da suka sanya gaba. Akwai kuma bukatar karfafa inganta yankunan.

Wakilai 123 na kasashen kungiyar, yankuna 1042 a jerin sunayen muhimmanci da yakai kilomita dubu dari 8 murabba'i, wasu kasashe cikin manufofi ko aiki a yankin. Kuma kasashen da suke da
kyawawan manufofi da tsarin aiki, sun samo asali ne daga taron. Wannan kuwa abin karfafa gwiwa neda taron na Ramser ya samar a yau.

Duk da haka bazamu sassauta ba. Dayawa daga cikin yankunan na Ramser na fuskantar barazana, akasarin basa samun kulawar da ta kamata. Wasu manufofin kula da irin wadan nan yankuna suna
kan takarda ne kawi, kuma yarjejeniyar ta Ramser a wasu kasashe basa da tasiri wajen tsara manufofi da aiwatar da harkokin gwamnati kamar yadda yakamata.

Domin magance wannan al'amari muna bukatar kara cusa mutane cikin yarjejeniyar ta Ramser.
Kana akwai bukatar mu kara taimakawa jama'a, domiin gano martabar yankuna masu dausayii
dakuma irin aikin su, domin samun karin wadandaa zamu dogara kan su, yayinda aka zo zaben 10
10 Page 11 12
Vol. 11 No. 25 February, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
11
Gwamnatocin da zasu yanke shawara kan albarkatun kasa. Wannan shine babban burin ranar dausayin
duniya ta shekara ta 2001, mai taken Dausayin duniya. ' abinda za a gano' a ranar 2 ga watan
Fabrairu 2001 rana ce da jama'a zasu gano al'abarkatun aiyukan yankuna masu dausayi. Tayin haka
za a bada gagarumar gudunmawa wajen tabbatar da lafiyar duniya, wanda itace gida yazuwa
yanzu.
delmur...

Sashin Yara
Maharbi 17mins.
Da sanyi safiya, Jamina ta tafi wajen kakan ta domin karbar zuma. Sai k suka bi tsuntsuwar dake kai
su wajen zuma da nisa cikin daji. 'Ina son ganin giwaye inji Jamina'. Kana ganin zamu gan su?. Idan
mukayi sa'a inji kakan nata. Ba a ganin Giwwaye sosai yanzu. Tun lokacin da maharba suka zo.

Maharba Inji Jamina. Ina son zama maharbiya, sai jamina tana wasan harbi. Tana kwaikwayo harbin
Giwa, takuma takali karkanda cikin daji takuma tinkari zaki mai alfahari. Sanan ta juya ta kalli kakan
ta. Amma kafin wanna lokaci tayi nisa cikin daji ta yadda bata ganin kakan nata da tsuntsuwar dake
kai su wurin zuma. Tayi ta kira amma shiru kake ji. Sai can cikin daji Jamina tayi wani sault. Sai wani
irin tsoro da fargaba suka fada zuciyar Jamina. Tayi shiru tana sauraron sautin ta daga kan ta sama.
Sai taga Angulaye suna shawagi a sama cikin zafin rana daga nan ta san ba lafiya. Kar kishiga daji ke
kadai iyayen ta suka taba ja mata kunne. Saidi sautin ya zama ba abinda zata kauda kai bane sai tayi
ta bin inda yake fitowa. Tayi ta tafiya cikin daji.... har sai da ta bullo sarari. Can ne ta tadda wata
karamar Giwa tana kokarin tada uwar ta amma abin ya faskara.

Maharbin shima kamar Jamina ne ya bace ne kuma ya tsorata. 'Kada kiyi kuka yarin ya Sai Jamina ta
kada kai wata kila sauran Giwayen suna kusa ne. Amma babu abinda take ji a kunnuwan ta sai kukan
kwari cikin zafin rana. Ta san dan Giwan ba zai rayu batare da uwar sa ba, tayi kokari kai shi gida
domin gano sauran dangi. Amma akan hanya dan Giwan ya firgita.

'Ni ba maharbiya bace' ta fadi a hankali. Haka tayi tyiwa dan giwan magana har sai da ya fara shafar
ta da hauren sa. Jamina sai ta tashi ta fara tafiya na dan wani taki. Dan giwan sai ya bita a hankali
cikin zafin rana. Nan take sai ruwan sama ya fara zuba giwan ya sami karfin jiki yayi ta bin ta. Wata
sa'an sai su zame kana suyi tangal-tangal su mike. Haka dai sukayi ta tafiya cikin kungurmin daji.
Yayinda saririn samaniya ya fara wartsakewa, sai Jamina tayi tunanin jin harrrgowwwar Giwaye.
Yayinda ta tsaya domin sauraro da kyau, sai taji ashe iska ce ke kadawa., Dan Giwan ya dauki
tsawon lokaci bai iya tafiya ba. Daga bisa cikin bacin rai yaci gaba da tafiya.

'In kin bace' inji kakan ta; sai kibi makiyaya da rana zasu yi miki jagora zuwa kogi. Gida na daga
bangare daya na kogin'. Ya dauki dogon lokaci kafin Jamina da Dan Giwan suka cimma garken jakin
dawa wadanda ke tsallakawa. Sai sukayi ta bin garken cikin zafin rana. Yayinda rana ta fara yin sanyi
akarshe dai suka isa bakin wani kogi. Amma daga cikin ruwa wani mugun ido na kallon su, sai
Jamina ta fara ji a jikin ta akwai hatsari. 11
11 Page 12 13
Vol. 11 No. 25 February, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
12
'Akwai hatsari mu ketare ta wannan wuri tace da dan Giwa' Kamata yayi muci gaba da tafiya.
yayinda Jamina ta juya tana zaton zata ga garken Giwaye, amma ba abinda ta gani sai manyan
bishiyoyin Akashiya wadanda ke ta kadawa cikin zafin rana. Jamina da Dan Giwa suka shirya cigaba
da tafiya, amma nan da nan Dan Giwan ya fara kashe kafa.

Dan taki gaba kadan, yace da Jamina. Amma ina ya gaji ainun. Yayinda Jamina ke jiran sa sai ta fara
tunanin uwar ta. In har zata iya kiran ta. 'Yanzu mutane zamu fara nuna damuwa, zasu kuma fara
neman ta. Sai ta shhhafi dan giwan a hankali. Baida uwar da zai kira ta. Amma duhun dake karatowa
ba uwar sa bace.

'Maharba, ta fadi cikin sassanyar murya. Jamina si taji yanzu ita ma ta zama abin da za ayi farutar ta.
Tayi addu'ar ganin Dan Giwan baiyi wani abu ba. Amman Dan giwan sai yaji a jikin sa akwai hatsari
sai yayi tsaye tit kamar dutse, har sai hatsarin ya shige.

Dare yayi duhu sai tsoro ya fara kama Jamina. Ta matsa kusa da Dan Giwan, ta rungume shi saboda
tsorata yayinda taji kukan wani abu dake tsananin jin yunwa.

Yayinda Jamina take jiran dayi farautar ta, sai ta sake tunani da maganar da kakanta ya taba yi mata,
'muddin kika shiga cikin hatsari' yace da ita 'kar ki fidda rai'.

Saboda haka Jamina ta na sauraron iyayen ta. Ta rufe idanun ta, tana tunanin su. Amma kuma ba
abindda take gani a idon zucci sai Giwaye. Zuciyar ta tuntuni tana ta tunanin su Giwayen ne. Gaton
haure da kakanta ya gani tun yana matashi. Katuwar inuwar.

Giwa na tafiya kamar dodonni dake ketare tsaunuka. Tana iya jin gurnanin su kus da ita. Yayinda ta
bude idanun ta sai taga ga Giwaye nan dayawa suna kewaye da ita kamar dai ta kira su ne cikin
mafarkin ta. Amma Jamina bata ji tsoro ba. 'dauki wannan dan ku' inji ta ku kula dashi'.

Yayinda alfijir ya keto, sai uwar Jamina ta same ta tana barci cikin ciyaw. Ana wasan harbi ne sai na
bace' inji Jamina cikin hannkali, yayinda ake cigiya a kauyen.
Paul gaerary in the book "The Hunter"

Dandano Jiran Rabo
Sheke ayar ka da wadan nan karin maganganu na Afrika da zasuyi wuyar mantuwa.
Kan Hikima
Karka zauna har yamma a gidan da ba zaka kwana ba.
Ethiopia

Kar ka zagi kada yayinda kake kusa da ruwa.
Uganda. 12
12 Page 13
Vol. 11 No. 25 February, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
13
Kan hakuri
Kaza bata kwarzanar kasa da kafafun ta biyu.
Zimbabwe.

Hakuri shine kwai babba dake kyankyashe kaji mai yawa.
Zimbabwe
More African Proverbs

... Kalma kan halittu.
Wanda ya dasa itace yana kaunar saura jama'a baya ga kan sa.
Thomas Fuller
1723

Katuna...
Zuciya kamar tsiro ne tana girma wurin da take so.
Zimbabwe
African Proverbs 13

Page Navigation Panel

1 2 3 4 5 6 7 8 9
10 11 12 13

 

© 2002 Communicating for Change. All Rights Reserved
Developed by George Mbuagbaw